1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kama daruruwan bakin haure a Libiya

October 3, 2021

An sake kama wasu 'yan kasashen Afirka da dama a Libiya wadanda ke kokarin shiga kasashen Turai ta barauniyar hanya, kamen kuma da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da shi.

https://p.dw.com/p/41CrB
Europa | Seenotrettung im Mittelmeer
Hoto: (Hannah Wallace Bowman/MSF/SOS Mediterranee/AP Photo/picture alliance

Masu gadin teku a Libiya, sun kama wani jirgin ruwan katako shake da bakin haure kimanin 500 wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Wannan shi ne kame na baya-bayan nan da aka yi na wasu da ke barin kasashensu na asali musamman Afirka domin shiga nahiyar Turai ala kulli halin.

Kamen ya faru ne kwanaki biyu bayan wani farmaki da jami'ai suka kai kan wasu bakin hauren akalla dubu hudu a yammacin kasar ta Libiya.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, UNHCR, ta ce an jibge bakin hauren da aka kama ranar Lahadi a wata matatar mai da ke a birnin Zawiya na kasar.

Kasar ta Libiya dai ta kasance wata cibiya da gallibin 'yan Afirka masu neman rayuwa a kasashen yamma ke bi domin shiga ta barauniyar hanya.