1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tuhumi dan Ostiraliya da laifukan cin zarafi 1,623

Abdul-raheem Hassan
August 1, 2023

Wani tsohon ma’aikacin kula da kananan yara dan kasar Ostireliya, na fuskantar laifuka 1,623 kan lalata da ‘yan mata 91 a shekaru sama da 15, hukumomi na zargin mutumin da nadar hotuna tsiraicin yaran a cikin wayarsa.

https://p.dw.com/p/4Ue1n
'Yan sandan Ostiraliya
Hoto: Richard Wainwright/AA/picture alliance

'Yan sandan Ostireliya sun tuhumi wani tsohon mai kula da yara da laifukan cin zarafi 1,623 kan wasu 'yan mata 91, hukumomin sun ce wannan shi ne laifuka mafi muni da tarihin kasar kusan shekaru 40.

Mutumin mai shekaru 45 a duniya, yana fuskantar daurin rai da rai. Mataimakiyar kwamishinan 'yan sandan Ostireliya Justine Gough na cewa "Muna zargin wadannan laifukan sun faru ne a cibiyoyin kula da yara guda 10 tsakanin 2007 da 2013 da 2018 zuwa 2022, da wasu wurare a 2013 da 2014, da kuma wata cibiya a Sydney tsakanin 2014 da 2017. Dukkan yaran da ake zargi da aikata laifin 'yan mata ne." a cewar Gough