1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar: Mutum 10 sun mutu a harin 'yan bindiga

Ramatu Garba Baba
March 25, 2021

Mutane kimanin goma ne aka tabbatar da sun mutu bayan wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai a wasu kauyuka biyu da ke karkashin yankin Tillabery a Kudu maso yammancin jamhuriyyar Nijar.

https://p.dw.com/p/3r5wP
Symbolbild | Niger Islamistischer Terrorismus
Kaburan wasu sojojin Nijar da mayakan jihadi suka halaka a can bayaHoto: Boureima Hama/Getty Images

Yanzu haka an tabbatar da mutuwar mutum akalla goma a wani sabon hari da ake zargin 'yan bindiga da kai wa, a wasu kauyuka da ke a yankin Tillaberi. Wani babban jami'in tsaron kasar, ya ce, maharan a yayin kai harin, sun kona wata makaranta da ke a kauyen Zibane inda a aka rasa rayuka uku sauran bakwai kuma a kauyen Gabado aka halaka su, ya baiyana fargabar karuwar alkaluman mamata a sakamakon harin na jiya Laraba.

Kawo yanzu dai,  ba a kai da gano wadanda keda hannu a harin da ke zuwa bayan wani munmunan harin da ya halaka mutum kimanin dari da talatin da bakwai a ranar Lahadin da ta gabata a yankin kudu maso yammancin jamhuriyyar ta Nijar ba. Hare-haren masu nasaba da aiyukan 'yan ta'adda, na zuwa ne a daidai lokacin da aka bude taron kasa da kasa kan batun inganta tsaro a kasashen yankin Sahel da na Tafkin Chadi, a Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar.