1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa Japan harin ta'addanci

Ramatu Garba Baba
July 18, 2019

A birnin Kyoto na kasar Japan, mutum akalla 33 aka tabbatar da mutuwarsu a sanadiyar wani harin ta'addanci da aka kai a wata masana'antar hada fina-finan majigi.

https://p.dw.com/p/3MGMd
Japan Brand in Filmstudio
Hoto: Getty Images/Jiji Press

Wani baban jamai'in 'yan sanda na yankin, ya ce wani mutum ne ya afka wa masana'antar inda bai yi wata-wata ba ya cinna mata wuta, ya kara da cewa, wannan shi ne karon farko da Japan ke rasa rayuka mai yawan gaske a lokaci guda a sanadiyar harin da tuni ake zargin na ta'addanci ne.


Wadanda suka sami raunin na cikin mawuyacin hali, abin da ya sa ake fargabar alkaluman mamatan ka iya haurawa. Shugaban masana'antar ya ce, daman  sun jima suna fuskantar barazana daga wurin wasu da ba asan ko su waye ba, da ke aiko musu sakonnin email akai akai.