1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai harin kunar bakin wake masallacin juma'a na Maiduguri.

July 13, 2012

Wani yaro dan kunar bakin wake ya kai hari da ya hallaka mutane biyar a masallacin juma'a na Maiduguri.

https://p.dw.com/p/15Xda
epa03095737 Nigerian boys sift through the remains of the Gamboru market after multiple explosions in Maiduguri, northern Nigeria, 07 February 2012. Three people have died in bomb blasts by the radical Islamist group Boko Haram in northern Nigeria, police said 07 February. Police told the German news agengy dpa that the owner of a pharmacy in the northeastern city of Maiduguri, and two of his employees, were killed when bombs went off. In the city of Kano, two police stations where Boko Haram members were being detained were also targeted. Police said there were no deaths. Boko Haram claimed responsibility for both attacks, which occurred as residents were observing Eid-el-Mulud, the Muslim festival marking the birth of the Prophet Mohammed. In the nearby town of Kaduna a man in military uniform was reported to have blew himself up outside an army barracks. Boko Haram Islamist militants have recently killed hundreds in bomb attacks across northern Nigeria. EPA/STR
Hoto: picture-alliance/dpa

A Najeriya wani dan kunar bakin wake ya kai hari wanda ya hallaka mutane biyar yayin da suke fitowa daga babban masallacin juma'a na Maiduguri dake kusa da fadar Shehu Borno bayan kammala sallar juma'a. Rahotanni sun ce mataimakin gwamnan jihar Borno Zanna Umar Mustapha da Shehun Borno Umar Garba el- Kanem da kuma wani babban malamin addinin musulunci sun tsallake rijiya da baya a wannan hari. An baiyana cewa dan kunar bakin waken yaro ne karami dan kimanin shekaru 15 da haihuwa. kakakin rundunar tsaro ta Soji a jihar Borno Kanar Sagir Musa yace akalla mutane shida sun sami raunuka. Babu dai wanda ya dauki alhakin kai wannan hari sai dai a Najeriyar hare hare makamancin wannan da kungiyar Ahlul Sunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram take kaiwa ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da dama.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi