1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na kara kamari a Libiya

Zulaiha Abubakar MNA
December 25, 2018

Wasu 'yan kunar bakin wake dauke da jigidar bama-bamai sun kai hari a ma'aikatar harkokin wajen kasar Libiya da ke Tripoli babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3AcXZ
Anschlag auf libysches Außenministerium
Hoto: Reuters/H. Amara

Jami'an tsaro a Libiya sun baiyana cewar bam ya tashi da guda daga cikin maharan bayan da suka yi nasarar harbe wani daga cikinsu.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta baiyana cewar ya zuwa wannan lokaci mutane tara na kwance asibiti suna karbar magani sakamakon muggan raunukan da suka samu bayan da wasu suka rasa rayukansu.

Kasar Libiya mai arzikin man fetur ta tsunduma cikin rikici tun daga lokacin da kungiyar tsaro ta NATO ta jagoranci kawo karshen mulkin shugaba kasar marigayi Moammar Gaddafi a shekara ta 2011.

Yanzu dai kasar na da shugabancin gudanarwa guda biyu daya a babban birnin kasar Tripoli wanda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi, yayin da bangare guda ke birnin Tobruk da ke gabashin kasar, baya ga gungun 'yan tawaye da ke hankoron karbe jagoranci da arzikin kasar.