1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan Asibitoci a Siriya

Abdul-raheem HassanJuly 24, 2016

Jiragen saman yaki sun kaddamara da hare-hare da ya rugur-guza asibotoci hudu a binirnin Aleppo da ke arewacin Siriya.

https://p.dw.com/p/1JVBV
Flugzeugträger Charles de Gaulle
Hoto: picture-alliance/abaca

Jiragen saman yaki sun kaddamara da hare-hare ta sama a kan asibotocin tafi da gidanka guda hudu a binin Aleppo dake arewacin Siriya. Jami'an kiwon lafiya sun ce harin yayi sanadiyar mutuwar jarirai biyu. Kungiyoyin sa ido a Siriya na ganin harin ka iya jefa rayuwar farafen hula sama da 200,000 da ke yankunan da 'yan tawaye ke iko da su. Likitoci ba sa iya gudanar da aikyukan ceto sakamakon lalata dakunan karin jini da karbar magunguna.

Birnin Aleppo ya sha fama da hare-haren jiragen yakin sama na hadin guiwar dakarun gwamnati da na Rasha. Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO, ta ce Siriya ta kasance kasa mafi hatsarin gaske ga jami'an kiwon lafiya da suka fuskanci hare-hare 135 a tun shekara ta 2015.