1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari a jami'ar Bayero ta Kano

April 28, 2012

Wasu mahara sun kai farmaki a jami'ar Bayero ta Kano, inda mutane da dama suka mutu wasu suka jikkata

https://p.dw.com/p/14mDE
A view of the old gate of Bayero University in Nigeria's northern city of Kano April 29, 2012. Gunmen killed at least 15 people and wounded many more on Sunday in an attack on a university theatre being used by Christian worshippers in Kano, a northern Nigerian city where hundreds have died in Islamist attacks this year. REUTERS/Stringer(NIGERIA - Tags: CRIME LAW)
Anschlag Nigeria Kano Bayero UniversitätHoto: Reuters

A ƙalla mutane 20 suka mutu yayin wani harin da aka kai a jami'ar Bayero ta Kano. Kamfanin dillalcin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kai harin ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da ibada wanda aka sabayi a babban dakin karatu na tsohowar BUK da safiyar yau. Rundunar soji dama jami'an yan sanda a birnin Kano sun tabbatar da kai harin, amma basu bada adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba kawo yanzu. Jami'ar Bayero dai tana da tsauraren matakan tsaro, domin a faɗar wani malami a jami'ar, idan mutun yaga irin binciken ƙwaƙwab da ake yi tun da ga ranar Juma'ar shekaran jiya, to zai yi mamaki ace mahara ɗauke da bama-bamai da bindigogi su samu shiga. Ganau suka ce maharan sun shiga da babura biyu da mota, inda suka fara buɗe wuta kan jama'a. An dai ji tashin bama-bamai da bindigogi tunda daga wajen jami'ar. kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.

A machine gun is seen on an armoured vehicle in front of Bayero University in Nigeria's northern city of Kano April 29, 2012. Gunmen killed at least 15 people and wounded many more on Sunday in an attack on a university theatre being used by Christian worshippers in Kano, a northern Nigerian city where hundreds have died in Islamist attacks this year. REUTERS/Stringer (NIGERIA - Tags: CRIME LAW)
Jami'an tsaro a KanoHoto: Reuters

Gabanin harin kan jami'ar Bayero

Hankali dai na dada tashi kuma zuciya tana shirin baki ga masu farautar labarai a tarrayar nigeria dake cikin tsaka mai wuya kuma ke kara fuskantar matsin lamba a kokarinsu na sauke nauyin aikin. A tsakanin gwamantin kasar da kuma yayan kungiyar boko haram din da suka kaddamar da wasu jerin hare hare akan kafafen yada labaran kasar 3.

Babu dai zato ba kuma tsammani aka wayi gari da hari kan wasu kafafen yada labaran kasar ta Najeriya uku a wani abun dake zaman sabon yanayi a cikin yakin ta'addancin da yaki ci yaki cinyewa kuma ke neman tsallakowa ya zuwa ga yan jaridar kasar ta Najeriya. Tuni dai kungiyar Boko haram mai fafutuka da boma bomai ta dauki alhakin shirin day a kai ga asarar rayuka akalla shida sannan kuma ya kai ga lalata offishin jaridar Thisday mai zaman kanta a nan Abuja. Kuma babbar hujja ta kai harin a cewar kungiyar na zaman rawar jaridun da rashin adalcin ga yanda suke baza labaran harkokin yakin ta'addancin kasar ta Nigeria.

Kungiyar dai na barazanar cigaba da kaddamar da harin kan kafafen yada labarai a cikin kasar ta Najeriya in har babu sauyin rawa a cikin abun da suka kira son raid a rashin adalci a cikin harkokin jaridun kasar ta Najeriya. Sabon harin dai na nuna irin jan aikin dake gaban mafarauta labaran kasar ta Najeriya dake tsaka mai wuya tsakanin kungiyar ta boko haramun da kuma gwamantin kasar dake zargin wasunsu da taimakawa aiyyukan kungiyar. Mr. labaran maku dai na zaman ministan yada labaran kasar ta Najeriya kuma kakakin gwamnatin ta.

This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Kakakin kungiyar Boko Haram Imam Abubakar ShekauHoto: AP

Ba zamu amince da amfani da kafafen yada labarai na waje a matsayin makamain furofagandar yan ta'adda a Najeriya. muna rokon duk kafafen yada labaran wajen dake aiyyukan su a Najeriya kar su bar kansu zama kafa ta yada matsayi na tsana da kiyayya a bangaren kungiyoyin yan ta'adda a tarayyar Nigeria.

Akalla yan jaridu biyu ne dai suka rasu sakamakon harin na boko haramun a cikin tsawon wattani 6 da suka gabata banda kuma jerin barazana iri iri ga kafafen yada labaran dama masu sana'ar ta jarida cikin kasar. Abun kuma dake kara jefa su cikin hali na gaba kura bayanta siyaki a kokarin kaiwa ga sauke nauyin sanar day an kasar dama bakin ta gaskiyar lamuran yakin day a hallaka daruruwan yan kasar kuma ke neman wucewa da sanin mahukuntanta.

epa03197097 Security officials gather at the site of a bomb blast at 'This Day' Newspaper office in Abuja, Nigeria, 26 April 2012. Newspaper offices in two Nigerian cities were targeted in coordinated bomb blasts, with several casualties reported, the authorities said. The offices of This Day newspaper in the capital Abuja and Kaduna city were attacked. At least one person was killed and many more were injured, officials said. Rescue workers gave conflicting accounts. Some said a suicide bomber blew up the newspaper's building in Abuja, while others said a bomb was planted at the office. The offices of newspapers Sun and Moment in Kaduna, north-central Nigeria, were also targeted in separate blasts. Four people are feared dead in those blasts and dozens injured, the authorities said. EPA/GEORGE ESIRI
Cikin ginin kamfanin jaridar This Day a AbujaHoto: picture-alliance/dpa

Shuaibu Leman dai na zaman sakataren kungiyar Yan jaridar kasar ta Nigeria ta NUJ.

Anan Abuja dai yan jaridar da yawa na cigaba da kauracewa ofisoshi da sauran wuraren aikin nasu a wani abun dake nuna alamar tsoro game da rayuwa dama makomar su cikin yakin. To sai dai kuma kowane irin tasiri sabon matsayin ke iya yi ga aikin na jarida dai a cewar Shu'aibu leman din tsoratar day an jaridar na iya shafar cigaban tsarin demokaradiya dama makomar kasar ta Nigeria baki dayanta. Abun jira a gani dai na zaman tasirin Karin matsin lamba gay an jaridar kasar ta Nigeria da suka yi kaurin sunan fadar na albarkacin baki komai daci a kasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman