1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati za ta dauki nauyin al'umma a Togo

Abdourahamane Hassane
April 2, 2020

Shugaban Togo Faure Gnassingbé ya kafa dokar ta baci ta tsawon watannin uku saboda  kiyaye yaduwar cutar Coronavirus wacce a halin yanzu ta kashe rayuka biyu a kasar.

https://p.dw.com/p/3aMss
Faure Gnassingbe
Hoto: AP

Gwamnatin ta Togo ta ce za ta kashe Euro milyan dari shida saboda daukar nauyin al'umma wadanda wasu za su rasa kudaden shiga saboda rashin aikin yi. Kasashen kungiyar tarrayar Turai dai na bayyana fargabansu game da dorewar 'yanci na dimukaradiyya sakamakon tsatsaurar dokoki da suka sabama tsari na dimukaradiyya da kasashe ke dauka saboda cutar wadanda suka bukaci da a yi sassauci.