1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban Somliya ya dauki madafun iko

Suleiman Babayo ATB
June 9, 2022

Sabon shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya nemi taimakon kasashen duniya domin magance matsalolin kasar.

https://p.dw.com/p/4CUuE
Somalia Hassan Sheikh Mohamud
Hoto: Abukar Mohamed Muhudin/AA/picture alliance

An kaddamar da sabon shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud wanda lokacin jawabi ya bukaci kasashen duniya su kara taimakon kasar magance matsaloli da suka hada da fari gami da tsaro.

Shi dai Hassan Sheikh Mohamud ya rike madafun iko daga shekara ta 2012 zuwa 2017 kafin ya sake dawowa ya lashe zaben da ya gabata.

Ita dai kasar Somaliya ta kwashe fiye da shekaru 30 cikin rikice-rikice na siyasa da yakin basasa da hargitsi masu ikirarin jihadi na kungiyar al-Shabaab.