1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu kamfanoni da birane sun fara rage hayaki mai guba

Zulaiha Abubakar
June 5, 2020

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da sabon shirin yaki da sauyin yanayi a wannan Juma'ar da ke ranar muhalli ta duniya, mai manufar kawo karshen fitar da hayaki mai guba.

https://p.dw.com/p/3dHyN
Symbolbild Klima
Hoto: Imago-Images/F. Gaertner

Wani rahoto da Majalisar ta fitar ya bayyana cewar kusan kamfanoni 1000 da birane 458 da yankuna gami da jami'oi da masana'antu sun fara rage fitar da hayakin da yake illata muhalli da nufin fara aiki da bukatar kawo karshen amfani da hayaki a shekara ta 2050.

Da yake karin haske game da wannan kudiri Alok Sharma wanda ke zaman shugaban da zai jagoranci babban taron sauyin yanayi mai zuwa ya bukaci sake tsarin tattalin arziki ta hayar dacewa da ingantacce kuma tsabtataccen muhalli bayan karshen annobar coronavirus.