An jinkirta batun fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai
December 17, 2018Majalisar dokokin Birtaniya za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar fita daga kungiyar Tarayyar Turai a tsakiyar watan gobe na Janairu na sabuwar shekara ta 2019. Firaminista Theresa May ta ayyana haka a wannan Litinin yayin muhawara a majalisar dokokin, wanda aka dakatar domin ci gaba da yi ranar 7 ga watan gobe na Janairu.
Idan majalisar ta koma muhawara 7 ga watan na Janairu sabuwar shekara ta 2019, mako guda daga bisani za a kada kuri'a kan batun na ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai. Lokacin tattaunawar jagoran 'yan adawa Jeremy Corbyn na jam'iyyar Labour ya caccaki Firaminista Theresa May saboda jinkirta kada kuri'ar a majalsiar dokokin ta Birtaniya. Akwai 'yan majalisa da dama na bangaren jam'iyya mai mulki ta Conservative gami da jam'iyyar adawa ta Labour da suka harzika kan matsayin gwamnatin Birtaniya a kan ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai da yadda firaminitar take jan kafa.