1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ja kunnen Sudan kan matsawa masu zanga-zanga

June 28, 2012

Hukumar kare haƙƙin bani adama ta Majalisa Ɗinkin Duniya ta gargaɗi Sudan kan muzgunawa masu shirya zanga-zanga

https://p.dw.com/p/15NaB
Hoto: AP

Shugabar hukumar kare haƙƙin bani adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya Navi Pillay ce ta yi wannan gargaɗi a alhamis ɗin nan gabannin wata gagarumar zanga-zanga da 'yan adawa za su yi a ƙasar a gobe Juma'ar nan.

Wannan jan kunnen na Uwargida Pillay dai na zuwa ne daidai lokacin da Amurka ke yin Allah wadai da ƙoƙarin mahukuntan Sudan na yin amfani da ƙarfin tuwo kan masu zanga-zanga ta hanyar tarwatsa su da barkonon tsohuwa da kuma harbi da harsasan roba, to sai dai mai magana da yawun ma'aikatar ƙasashen ƙetare ta Sudan ɗin Al-Obaid Adam Marawih ya ce magana da Amurka ta yi katsalandan ne kan harkokin cikin gidan Sudan ɗin.

Amurkan dai da sauran ƙasashen duniya sun ce maimakon amfani da ƙarfi kan masu zanga-zanga, kyautuwa ya yi a zauna kan teburin shawarwari da nufin jin koken masu zanga-zangar don warware komai cikin laluma.

Mutane ne da dama dai waɗanda su ka haɗa da masu rajin kare haƙƙin bani adama da 'yan jarida da kuma ɗalibai gami da 'yan adawa mahukuntan na Sudan su ke tsare da su sakamakon nuna adawarsu game da matakan tsuke bakin aljihun da kuma rashin bada damar gudanar da harkokin siyasa a ƙasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu