An harbe sojojin NATO uku a Afghanistan
June 8, 2013Talla
A wata sanarwa da NATO ta fitar a wannan Asabar din ta ce mutumin da yi ya yi kisan na daga cikin wadanda jami'an na NATO ke bawa horo a kasar.
Kawo yanzu dai rundunar ba ta yi wani karin haske ba game da asalin kasashen da wadannan mutane da aka kashe su ka fito.
NATO dai ta kara da cewar za ta yi bayani ne bayan ta kammala tattaunawa da mahukuntan kasashen da jami'an da su ka riga mu gidan gaskiya su ka fito to sai dai rahotanni na cewar galibin jami'an na NATO da ke aiki a yanki da aka yi kisan Amurkawa ne.
Mwallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman