1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai Turkawa masu yawa a Jamus da Sweden

Zainab Mohammed Abubakar
June 21, 2018

Turkiyya ta hana 'yan majalisar Turai biyu shiga kasar a matsayin wakilan sa ido daga Turai, batu da ke dasa ayar tambaya dangane da adalci a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da ke tafe ranar Lahadi

https://p.dw.com/p/302tk
Türkei Kundgebung zur Unterstützung von Erdogan in Istanbul
Hoto: Reuters/O. Orsal

Ana saran Tayyip Erdogan zai sake lashe zaben Lahadin, bayan nan a bawa shugaban kasar sabbin madafan iko. Tuni dai rigingimu suka mamaye yakin neman zabe, a yayin da 'yan adawa suka koka da rashin basu damar amfani da kafofin yada labarun kasar.

Haramtawa 'yan majalisar Jamus da Sweden da ke zama kasashe biyu da ke da  mafi yawan al'ummar Turkawa a Turai, zai kara assasa damuwa a zukatan kungiyoyin kare hakkin jama'a dangane da yiwuwar yin magudi, saboda babu masu sa ido.