1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Madugun adawa ya gaza shiga kasar

August 3, 2018

Hukumomi sun hana madugun adawar Kwango Moise Katumbi shiga kasarsa a kokarin da ya ke yi na zuwa neman takara.

https://p.dw.com/p/32bXN
Moise Katumbi Chapwe Kongo
Hoto: Getty Images/F. Scoppa

Shi dai Mr. Katumbi wanda hamshakin dan kasuwa ne, an dakatar da shi daga shiga kasar ne a kan iyakar kasar da Zambiya. Dan siyasan wanda tsohon gwamna ne a yankin Katanga, na zaune ne a kasar Beljiyam tun cikin watan Mayun shekara ta 2016, bayan takaddama tsakaninsa da Shugaba Joseph Kabila.

A wannan makon ne ma wani babban mai adawa da Shugaba Kabilan wato tsohon mataimakain shugaban kasa Jean-Pierre Bemba ya koma kasar ya kuma bayyana takararsa ta shugabancin kasa a ranar Alhamis da ta gabata. Shi dai Shugaba Joseph Kabila na jagorantar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon ne tun a shekara ta 2001.