1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka masu zanga-zanga a kasar Benin

April 8, 2021

Wani harin jamia'an tsaro ya haddasa zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutun guda tare da jikka wasu da dama a jamhuriyar Benin.

https://p.dw.com/p/3rjG0
Weltspiegel 08.04.21 | Benin | Demonstranten gegen Präsident Talon errichten Straßensprerren
Hoto: Yanick Folly/AFP

Shugaba Patrice Talon na jamhuriyar Benin da ya yi alkawarin yin wa'adin guda a jagorancin kasar bayan zabensa a shekara ta 2016, ya kara kutsa kansa a jerin yan takara a babban zaben kasar da ake shirin gudanarwa Lahadi mai zuwa, wanda ya haddasa zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutun guda tare da jikka wasu mutane shidda a yau din nan.

Talon ya ce bukatar hakan ta bijiro ne sakamakon abin da ya ke son yi na karasa manyan ayyukan da ya fara, da suka hada da zamanatar da yadda ake tafiyar da gwamnati da kuma kirkiro wasu sabbin hanyoyin sama wa kasar kudaden shiga da ya yi da kaso 5 cikin dari, bayan da Benin din ta zama ta farko a yammacin Afirka wajen noman Auduga.

Sai dai an zargi shugaban da takura wa manyan masu hamayya da shi yin gudun hijira, bayan gwamnatin ta zargesu da alaka da ayyukan ta'adanci. Alassane Soumanou tsohon jami'i a gwamnatin Yayi Boni da Corentin Kohoue wani dan siyasa, sun kasance yan adawar da hukumar zabe ta ki amincewa da takararsu tare da tilasta masu barin kasar.