1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro sun mutu a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
June 11, 2021

Wani harin 'yan bindiga a Jamhuriyar Nijar ya hallaka jami'an tsaron kasar hudu a yayin da suke sintiri a saharar garin Assamaka da ke kan iyakar kasar da Aljeriya.

https://p.dw.com/p/3ujvk
Niger Polizei in Niamey
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

'Yan sanda uku da wani genderme guda ne suka game da ajalinsu, biyo bayan harin 'yan bindigar da ya auku lokacin da suke sintiri a yankin saharar da ke tsakanin kasashen Nijar da Aljeriya.

Ma'aikatar cikin gidan kasar da ta tabbatar da harin a cikin wata sanarwa, ta kuma bayyana a yammacin jiya da cewa, jami'anta sun yi nasarar fatattakar maharan tare lalata motocinsu, jim kadan bayan kai farmakin na Assamaka da ke Arewa maso yammacin kasar.

Ko a shekarar 2017 ma dai, rahotanni sun ce jami'an Nijar biyar ne a jimmalace suka mutu a yankin mai iyaka da Aljeriya, yankin da ta nan ne Aljeriyar ke dawo da dubban 'yan ci-rani da bakin haure da ke shigewa ta kasar ba tare da ka'ida ba.