Thailand: Hari ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro
November 6, 2019Talla
Rahotanni sun ce an kai harin ne kan wani shingen jami'an tsaron a lardin Yala tare da wasu ababen fashewa, lamarin da kakakin rundunar tsaron yankin Kanal Pramote ya kira da aiyukan ta'addanci ne.Tun a shekarar 2004 ne dai lardunan da ke kudancin kasar Thailand da suka hada da Pattani da Narathiwat da Yala ke fama da hare-haren kungiyoyi sa kai masu gwagwarmaya da makamai, wadanda ake zargin cewa na tsananin kishin addinin Islama ne ke kai harin inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu bwakai.