1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSomaliya

Somaliland: Zaben shugaban kasa cikin tashin hankali

Abdourahamane Hassane
November 13, 2024

Al ummar kasar Somaliland na kada kuri'a a wani muhimmin lokaci a tarihinta,na neman amincewar kasashen duniya wadanda suka mayar da ita saniyar ware.

https://p.dw.com/p/4mx8d
Somalia Mogadischu | Menschen auf Straße während Kämpfen zwischen Regierungstruppen und Oppositionstruppen
Hoto: Feisal Omar/REUTERS

 Masu kada kuri'a miliyan miliyan daya da dubu 22 za su zabi tsakanin shugaban kasa mai barin gado,shugaban babbar jam'iyyar adawa Abdirahman Mohamed Abdullahi, da kuma shugaban jam'iyyar Social Justice Party (UCID) Faysal Ali Warabe. Tun farko an so shirya gudanar da zaben a shekara ta 2022, amma aka dageshi saboda dalilan rashin kudi. Amma 'yan  adawa sun yi tir da lamarin kan cewar shugaban na neman tsawaita  wa'adin mulkinsa