1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta kasa dakatar da yakin Gaza saboda kin yardar Amurka

Abdourahamane Hassane
December 9, 2023

Amurka ta ki amincewa da wani kuduri na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita bude wuta na jin kai cikin gaggawa a Gaza, duk kuwa da matsin lamba daga babban sakataren MDD na tsagaita wutar.

https://p.dw.com/p/4Zxig
Hoto: Yuki Iwamura/AFP/Getty Images

 Kwamitin sulhun na MDD ya gaza cimma matsaya wajen amincewa da kudirin a taron da ya yi, bayan da  Amirka ta  hau kujera  naki kan dakatar da yakin. Yakin da aka shafe watanni biyu ana gwabzawa tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas ya kasara al'amura baki daya a yanki. A halin da ake ci ana cigaba  da gwabza kazamin fada daga arewa zuwa kudancin zirin Gaza, musamman a Khan Younes, babban birnin kudancin kasar, inda sojojin Isra'ila suka sanar da cewa sun ja dagga kuma suna bi gida- gida domin zakulo mayakan Hamas. Al'ummar da ke fuskantar wani mummunan yanayi, an tilasta musu ƙaura a cikin wani yanki mai cike da cunkoso zuwa Rafah, da ke kan iyaka da Masar, inda  dubban mutanesuka samu mafaka a sansanonin wucin gadi. Wadanda suka tsira daga tashin bama-bamai a halin yanzu suna cikin hadarin mutuwa saboda yunwa da cututtuka,in ji kungiyar  Save the Children