An gargadi al'ummar Masar da su guji tada rikici
July 22, 2013Majalisar ministocin ta yi wannan gargadi ne yayin taronta na farko da ta gudanar a wannan Lahadi (21.07.13) inda ta yi kira ga al'ummar kasar da su bada gudumawarsu ga sabon kwamitin da aka girka a kasar wanda zai yi garambawul ga kundin tsarin mulkin Masar din gabannin zaben 'yan majalisun dokokin kasar.
A daura da wannan, wani tashin hankali da aka samu a kasar ta Masar ya yi sanadiyyar kisan wasu sojoji biyu da dan sanda guda a yankin nan na Sinai yayin da daruruwan mata suka yi wani maci zuwa ma'aikatar tsaron kasar domin nuna fushinsu sakamakon kisan wasu mata uku da aka yi a wani gangami da magoya bayan hambararren shugaban Masar din Muhammad Mursi su ka yi a Mansura a ranar Juma'ar da ta gabata.
Zanga-zanga a Masar dai a dan tsakanin nan ta zama tamkar jamfa a Jos tun bayan da sojin kasar su ka hambarar da gwamnatin Mursi daga gadon mulki a farkon wannan watan.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh