1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano wata bam a ƙasar Masar

January 6, 2011

Hukumomi a ƙasar Masar sun ƙarfafa matakan tsaro gabannin bikin krismeti na yan 'ɗariƙar Coptik.

https://p.dw.com/p/zuSL
Hoto: AP

'Yan sanda a ƙasar Masar sun ce sun gano wata bam ƙirar gargajiya a cikin wata majami'ar da ke da ratan kilomita 200 daga kudancin birni Alƙahira. A jajibirin da mabiya ɗariƙar Coptik ke shirin gudanar da bukukuwan Sallah krimeti a gobe juma'a.

'Yan sanda sun ce abin da ka iya fashewar ya na cikin wani gwangwani madara gari da aka tsa tsake da abubuwan kayan wasan wuta dakuma ƙusoshi da suka samu a jikin matatakalar cocin.Haka dai ya zo ne ƙasa da mako ɗaya da kai wasu hare hare a Allexandria wanda a cikinsu mutane 21 suka mutu a wajan wani wurin ibada.Gwamnati a ƙasar ta Masar ta zuba sama da jami'an tsaro dubu 70 domin kiyaye al' amuran tsaro a shirin bukukuwan yan ɗariƙar coptik da ake somawa tun a marecen yau.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal