1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama masu satar zabe a Girka

Abdourahamane Hassane
May 21, 2023

An kama mutane biyar a arewacin Girka bisa yunkurin magudin zabe,yayin da al'umma ke kada kuri'ar a zaben 'yan majalisar dokoki. Jam'iyyun siyasa da dama ke fafatawa a zaben.

https://p.dw.com/p/4RdFi
Kyriakos Mitsotakis firaministan Girka mai barin gado
Kyriakos Mitsotakis firaministan Girka mai barin gado Hoto: Louiza Vradi/REUTERS

Ana ganin za a fi yin karon batar karfe tsakanin jam'iyyar 'yan mazan jiya ta New Democracy ta firaminsta mai barin gado Kyriakos Mitsotakis da jam'iyyar Syriza mai ra'ayin gurguzu ta tsohon firaministan Alexis Tsipras. Hasashe na baya- bayan nan da wasu kafofin suka bayyana na nuna cewar jam'iyyar New democracy ta firaministan mai ci yanzu na kan gaba, da yawan kuriu, amma kuma bala'in hadarin jirgin kasa na watan Fabrairu da ya afku a kasar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 57 ya ragewa firaminista kwarjini sossai a idon jamaar kasar.