1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano bama-bamai a jami'ar Bayero

May 8, 2012

An sami rudami da tsoro daga jama'a sakamakon binciko bama-bamai a Kano

https://p.dw.com/p/14rvc
Hoto: Reuters

Rundunar sojin Najeriya a jihar Kano ta sami nasarar kwance wasu bama bamai a harabar jami'ar Bayero dake Kano. Tun sanyin safiyar Talata ne dai aka fara kururuwar ganin wadannan bama bamai da aka ajiye a wasu sassan jihar, lamarin da yasa aka gayyato jami'an tsaro.

Wasu dalibai ne suka fara gano wadannan abubuwa da aka ajiye a harabar tsangayar koyon aikin likita da kuma ta koyon aikin lauya dake harabar tsohuwar jami'ar Bayero, daga bisani ne kuma bayan zuwan jami'an tsaro aka tabbatar cewar wadannan abubuwa bama bamai ne. Nan take dai aka shiga kokarin yadda za'a kwance su. Rundunar sojin dai ta kwance wasu daga cikin bama baman, ba tare da sun fashe ba, to amma duk da wannan kokari akwai wasu bama bamai 2 da ala dole sai da aka dauko su aka kaisu filin motsa jiki na jami'ar daga bisani kuma aka harbe su suka fashe kuma karar fashewar tasu ta haddasa rudani da guje guje.

Wasu mutane da suke cikin jamiar lokacin da abin ke faruwa sun bayyana yadda abin ya faru:

Tun lokacin da aka gano wadannan abubuwa sojoji suka mamye jami'ar ana cigaba da neman wasu bama baman. Hankulan mutane dai ya tashi matuka, inda kowa ke zuwa domin daukar yara dake karatu a makarantun dake cikin harabar jamiar, inda ake shan kwarbai da jami'an tsaron jamiar dake hana mutane shiga

Anschlag Nigeria Kano Bayero Universität
Tsoro a jami'ar Bayero a KanoHoto: REUTERS

Wani tsohon ma aikacin jamiar da aka hana shiga yayi bayani akan wannan batu

Musatapha Zaharaddeen shine jami'in hulda da jama a na jamiar ta Bayero ya bayyana min cewa an gano wadannan bama bamai ne tun da sanyin safiya daga bisani kuma aka gayyato jamian tsaro domin kwance su ya kyuma tabbatar da cewar sojojin sun fasa wasu bama baman tare da kwance wasu.

A waje guda kuma a jiya ne sojoji suka kai sumamme kasuwar wayar hannu dake yankin Sabon Gari, inda suka ringa shiga shagauna suna kama masu sayar kayan wayar salula. Wani daga cikin wadanda aka shiga rumfarsu a kasuwar ya bayyana yadda yasha da kyar a hannun wadannan sojoji

Anschlag Nigeria Kano
Matakan tsaro a arewacin NajeriyaHoto: Reuters

Sai dai har wannan lokaci kakakin rundunar sojin kasar ajihar kano baice komai ba akan wannan batu.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Umaru Aliyu