1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kwashe 'yan Sudan ta Kudu daga Sudan

May 14, 2012

Da safiyar litinin ɗin nan ce aka fara kwashe kason farko na 'yan Sudan ta Kudu da ke zaune a Sudan bayan da mahukuntan Khartoum su ka umarce su da su fice.

https://p.dw.com/p/14v8A
Süd Sudan Präsident Salva KiirHoto: picture-alliance/dpa

Jirgin farko na mutanen ya bar Sudan da sanyin safiyar yau inda ya sauka da mutane ɗari da sittin da shidda a filin jirgin saman Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.

Da ya ke jawabi game da wannan batu, ministan da ke kula da sha'anin jin daɗin al'umma Joseph Lual Acuil wanda ya isa filin jirgin saman don tarar jama'ar da su ka sauka ya bayyana jin dadinsa game da isar mutanen gida.

Wannan kason da su ka sauka a yau dai na daga cikin mutane dubu sha biyar ɗin da yanzu haka za a kwashe daga Sudan zuwa Sudan ta Kudu.

Kwashe al'ummar dai ta biyo bayan sanya wa'adin ranar ashirin ga wannan watan da mu ke ciki don 'yan kasar ta Sudan ta Kudu su fice daga Sudan domin ita Sudan na daukar zaman 'yan Sudan ta Kudun a ƙasar ta a matsayin wata barazana ta tsaro.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh