1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kwashe majinyata a asibitin al-Shifa

Abdourahamane Hassane
November 21, 2023

Asusu yara kanana na MMD UNICEF ya yi gargadin cewar wani mummunan bala'i na kiwon lafiya na kunno kai a yankin zirin Gaza, saboda rashin man fetur da ruwa.

https://p.dw.com/p/4ZHIY
Hoto: Hatem Khaled/REUTERS

Kakakin hukumar na UNICEF James Elder ya shaida wa manema labarai a Geneva cewar, idan babu isasshen man fetur, ayyukan tsaftar muhalli za su  ruguje. Akwai kuma barazanar kamuwa da cutar amai da gudawa a yankin na zirin Gaza inda jama'a suka cika asibitoci makil da masu jinya.

Yanzu haka dai an fara kwashe majinyata a asibitin al-Shifa, wanda shi ne mafi girma a Gaza. Yayin da  wasu asibitoci biyu da ke arewacin Gazan asibitin Indonesiya da kuma asibitin Ahli Arab, suma suka bukaci taimako daga hukumar lafiya ta duniya domin saukaka kwashe mutanen.