1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kokarin kafa gwamnatin riko a Burkina Faso

October 15, 2022

Shugabannin sojoji da 'yan siyasa gami da wakilan kungiyoyin fararen hula a Burkina Faso, sun fara wani taro a jiya Juma'a da nufin sama wa kasar shugaba na riko kwarya.

https://p.dw.com/p/4IEOX
Burkina Faso l Nationale Konferenz : les Assises nationales de la transition, Ouagadougou
Hoto: Service d'information du gouvernement du Burkina Faso

Kimanin wakilai 300 ne dai za su hadu a Ougadougou babban birnin kasar ta Burkina Faso domin nazarin yadda za a maida kasar bisa tsari irin na dimukuradiyya.

Akwai dai yiwuwar Keftin Tarore wanda ya kifar da gwamnatin Kanal Henri Damiba a ranar 30 ga watan jiya na Satumba da ne za a bayyana a matsayin shugaban kasar na riko.

Cikin watan Janairun bana ne dai, shi ma Kanal Damiba ya hambarar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kaboré da tsinin bindiga saboda zargin gazawa wajen iya murkushe ta'addanci a kasar.

Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirka ECOWAS, na ci gaba da nuna damuwa kan hadarin subucewar dimukuradiyya a Burkina Fason.