1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Zaben kananan hukumomi ya gudana lafiya

December 13, 2020

An fara kidaya kuri'u a Jamhuriyar Nijar bayan da masu kada kuri'a suka gudanar da zaben kananan hukumomi domin sabunta kujerun kansaloli da na wakilan zauren shawara na jihohin Jamhuriyar Nijar,

https://p.dw.com/p/3mf2j
Niger Wahllokal in Niamey
Hoto: Reuters/J. Penney

Wasu rahotanni na nuni da cewa an rufe rumfunan ne da karfe 6 na yammacin Lahadi kamar yadda hukumar zaben kasar ta CENI ta umurta, yayin da aka tsawaita a runfunan da kayan zabe ba su isa da wuri ba. Haka kuma zaben ya gudana lami lafiya duk kuwa da barazanar tsaro da wasu yankunan kasar ke fuskanta.

Zaben na zuwa ne makonni biyu gabanin babban zaben kasar na shugaban kasa da na 'yan majalisa, inda ake sa ran mika ragamar mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata a karon farko cikin tarihin kasar. Shugaba Mahamadou Issoufou na daf da kammala wa'adinsa karo na biyu, sai dai ya yi tsayin daka kan sai dan takarar jam'iyyarsa da PNDS Bazoum Mohamed ya kai labari.