1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi kashedi ga Hong Kong

Abdourahamane Hassane
July 31, 2020

Jamus ta ba da sanarwar dakatar da yarjejeniyar da ke tsakanin ta da Hong Kong ta tisa keyar wadanda ake zargi da aikata laifuka bayan da China ta dage zaben da aka shirya yi a yankin.

https://p.dw.com/p/3gFXU
Firaministar Hong Kong  Carrie Lam
Firaministar Hong Kong Carrie Lam Hoto: Getty Images/AFP/A. Wallace

A cikin wata sanarwa da ministan harkokin waje na Jamus Heiko Maas ya bayyana ya ce dage zaben da shekara guda saboda corona. Bayan da aka haramta wa 'yan takarar jam'iyyar masu fafutukar neman sauyin na demukaradiyya tsayawa takara tare da kama wasu shugabannin kungiyoyin dalibai da kuma tilasta wa jagoran 'yan adawar yin hijira. Wani abu ne da ke zaman karan tsaye ga yankin wanda ke fafutukar neman 'yanci daga China domin tabbatar da tsari na demukaradiyya.