1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta dage zaben gwamnoni da mako guda

Uwais Abubakar Idris
March 9, 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da mako guda, saboda rashin lokacin da zata sake tsara bayanan da ke cikin naurar BVAS.

https://p.dw.com/p/4OQPi
Shugabnan INEC Mahmood Yakubu
Shugabnan INEC Mahmood YakubuHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Murna ce dai ta koma ciki ga masu doki da zumudin za'a gudanar da zaben gwamnonin jihohi.. da ‘yan majalisun dokokin na jihohin, abinda ya sanya sanar da dage zabubbukan ya jefa ‘yan kasar da dama cikin mamaki.

Hukumar zaben mai zaman kanta ta sanar da kara mako guda ne daga ranar 11 ga watan da za'a yi zabe yanzu an maida shi ranar 18 ga wata.  Amma me ya zafi bayan hukumar zaben ta samu nasara inda kotu ta bata umurnin saker tsara bayanan a naurorin tantance masu zabe ta Bvas haka katsam ta dauki wannan saboda mataki?

Koda yake dage lokacin da za'a gudanar da zaben batu ne da ya shafi daukacin jam'iyyun siyasu 18 na kasar da ke cikin zaben, amma jam'iyyar Labour it ace kan gaba wacce ta je kotu a kan batun da ya haifar da wannan sauyi. 

Najeriya dai ta dade tana fusknatar yawan dage zabubbuka. A 2011 har an fara jefa kuri'a a zaben shugaban Najeriyar kafin aka dagatar da shi, a 2018 da 2019 duka an dage zabukan gashi yanzu a 2023. Ta kaiga ana zargin ana hakan ne don taimakawa wasu jam'iyyun siyasa.

A yanzu jamiyyun siyasun Najeriyar sun samu karin lokaci na yakin neman zabe har zuwa daren 16 ga watan nan, kari da ga wasu jamyyun na jan aiki ne domin an dade ana yakin meman zabe da ke zukar kudi a yanayi na karanci da ma wahalar samun kudin a hannu.