1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An daba wa Salman Rushdie wuka a Amirka

Abdoulaye Mamane Amadou
August 12, 2022

Wani mahari ya kai wa Salman Rushdie hari da wuka a yayin da yake halartar taro a New-York na Amirka. Shi marubucin adabin ne jagoran juyin-juya halin Iran ya halasta jininsa bayan batanci ga annabi Muhammad (SAW).

https://p.dw.com/p/4FTmS
Salman Rushdie Schriftsteller
Hoto: Alexandre Marchi/MAXPPP/dpa/picture alliance

An kai wa marbucin nan dan kasar Birtaniya Salman Rushdie hari da wuka a yayin da yake halartar wani taro a yammacin birnin New York na kasar Amirka. Salman Rushdie dai ya shafe tsawon shekaru yana wasan buya, bayan da jagoran juyin-juyin halin Iran Ayatollah Rouhollah Khomeiny ya fitar da fatawar cewa jininsa ya halarta a shekarar 1989, bisa rubutun batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da ya yi.

Wani mahari ne dai ya dabawa Mista Rushdie wuka a wuya a yayin da yake dakon ya gabatar da jawabi a yayin taron na yammcin New York, kana nan take aka garzaya da shi zuwa a asibiti, sai dai ba a yi wani karin haske kan cikakkiyar lafiyarsa ba, sai dai rundunar 'yan sandan Amirka tuni ta tabbatar da kama maharin a wannan yammaci.