1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin Burundi da yan tawayen FNL

Zainab A MohammedJune 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6V

A jiya ne gwamnatin Burundi ta rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu da kungiyar tawaye ta karshe data ki bada hadin kai a baya.Kungiyar ta FNL da gwamnatin burundin sun cimma wannan yarjejeniya ne a birnin Darussalam din kasar Tanzania,wanda ya kawo karshen tashe tashen hankula day a jefa kasar yakin basasan shekaru 13.Bayan rattaba hannu a yarjejeniyar sulhun shugaban kasar Tanzaniya kuma mai masaukin bakin wannan tattaunawan sulhu,Jakaya Kikwete ya bayyana farin cikinsa dangane da wannan matsaya da bangarorin biyu dake adawa da juna suka cimma bayan lokaci mai tsawo.

“Muna matukar farin cikin ganin cewa harkokin siyasar kasar Burundi ya fara daukan managacin salo.Munyi maraba da wannan zartarwa na dakatar da dukkan tashe tashen hankula,wanda ya jagoranci yarjejeniyar tsagaita wuta.”