1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An ceto wasu bakin haure a Italiya

January 22, 2022

An ceto wasu daruruwan bakin hauren da ke neman kutsawa nahiyar Turai ta karfin tsiya. Wadanda aka ceton dai sun fito ne daga kananan kasashe masu fama da talauci.

https://p.dw.com/p/45wXk
Europa | Seenotrettung im Mittelmeer
Hoto: Renata Brito/AP Photo/picture alliance

Masu gadin kan teku a Italiya, sun ceto wasu bakin haure sama da 300 wadanda ke kan hanyarsu ta neman shiga nahiyar Turai ba bisa ka'ida ba.

Jirgin ruwa da ke dauke da mutanen da galibin su suka fito daga kasashen Afirka da ma wasu na Asiya, ya fusknci matsala a tsibirin Lampedusa.

Daga cikin wadanda aka ceto dai har da mata 17 da kananan yara shida.

Masu gadin na kan tekun, sun shaidar da samun matsalolin a kokarinsu na ceto mutanen saboda yawan su da kuma kankantar jirgin da ya kwaso su.

Sun ma ce mutanen na gab da fuskantar hadarin nitsewa saboda fashewar jirgin ka iya yi.

Kungiyar likitoci masu ba da agaji ta Doctors without Borders, ta ce jirgin na dauke ne da bakin haure 430.