1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto bakin haure a Sudan

September 12, 2018

Jami'ai a Sudan, sun ce sun ceto kimanin mutum 100 cikinsu har da mata da kananan yara, da ake kokarin safararsu zuwa wasu kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/34iRc
Libyen Tripolis Kämpfe zwischen Milizen
Hoto: Reuters/H. Amara

'Yan sandan kasar wadanda su ne suka tabbatar da wannan labarin, sun ce yayin wani sintiri na musamman da suka gudanar, sun kamo mutum 95, cikinsu kananan yara 85 daga hannun wasu bata-garin a Khartoum babban birnin kasar.

Ita ma rundunar 'yan sanda ta kasa-da-kasa wato Interpol, ta ce daga cikin yaran akwai wadanda aka tilasta wa shiga aikin hakar zinari a Sudan din.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa wadanda aka kaman na kokari ne na zuwa nahiyar Turai ta barauniyar hanya.

Mutanen dai sun fito ne daga kasashen Chadi da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Irititriya da Nijar da kuma Sudan ta Kudu.