1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen: An nemi tsagaita wuta

Ahmed Salisu
June 14, 2018

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zama na gaggawa a yau Alhamis inda ya duba batun yunkurin dakarun kwancen da Saudiyya na karbe iko da tashar jiragen ruwan nan ta Hodeida da ke kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/2zapc
Jemen Regierungstruppen starten Offensive zur Rückeroberung Hodeidas
Hoto: Getty Images/AFP/N. Hassan

Yayin zaman wanda ya gudana cikin sirri, kasashe duniya sun bukaci da a dakatar da barin wuta don bada dama ta tattaunawa da 'yan tawayen Houthi da nufin ganin sun fice daga yankin. Jakadun da suka halarci zaman suka ce dakatar da yakin ya zama wajibi muddin ana son kauracewa jefa fararen hula cikin halin kunci kasancewar da ita wannan tashar jiragen ruwa ake amfani wajen shigar musu da abinci da magunguna.