1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude sabon ofishin Majalisar dinkin duniya a birnin Bonn

July 11, 2006

Birnin Bonn Hedikwatar tsohuwar tarayyar Jamus ya karbi lakabin kasancewa birnin Majalisar dinkin duniya

https://p.dw.com/p/BtzF
Shugabar Gwamnatin Jamus Abgela Merkel tare da Sakataren Majalisar dinkin duniya KOfi Annan ke kaddamar da sabon ofishin MDD a birnin Bonn
Shugabar Gwamnatin Jamus Abgela Merkel tare da Sakataren Majalisar dinkin duniya KOfi Annan ke kaddamar da sabon ofishin MDD a birnin BonnHoto: AP

Sabuwar tsangayar majalisar dinkin duniyar wadda aka tsugunar a tsohuwar majalisar dokokin tarayyar Jamus dake kusa da tashar DW a nan birnin Bonn a yanzu zai kasance mazauni ga hukumomin majalisar dinkin duniya guda goma sha biyu wadanda ada suke sassa daban daban na birnin Bonn.

Da yake jawabi yayin bude cibiyar Sakataren majalisar dinkin duniyar Kofi Annan ya tunato da cewa tun a shekarar 1996 birnin Bonn ya karbi lakabin kasancewa birnin Majalisar dinkin duniya a hukumance kuma cibiyar muhawara ta kasa da kasa a game da muhimman batutuwa na kyautatuwar cigaba. Yace ginshikin daukakar kasa da kasa da birnin Bonn ya samu, ya samo asali ne bayan yarjejeniyar da aka sanyawa hannu a birnin Berlin a shekarar 1994 wanda ya zaiyana namijin aiki na raya birnin Bonn don kasancewa cibiyar raya manufofin cigaba kuma mazauni ga kungiyoyi da kuma hukumomi na kasa da kasa.

An kuwa dabbaka wannan cigaba ne tare da fara tsugunar da wasu muhimman hukumomi daga Berlin zuwa Bonn wadanda suka hada da hukumar raya kasa ta Inwent da hukumar taimakon kasashe masu tasowa DED da cibiyar nazarin manufofi ta Jamus DIE da kuma kungiyar hadin gwiwa da cigaban kasashe wadanda dukkanin su suka bude ofisoshin su a nan birnin Bonn tare kuma da cibiyoyin binciken kimiyya da kungiyoyi na gwamnati da masu zaman kan su a kalla guda 150 dake aiki da takwarorin su na kasa da kasa domin cigaban kasashe na duniya ta fannoni da dama.

Gwamnatin tarayyar Jamus ta kashe tsabar kudi euro miliyan 55 wajen gyaran sabon ofishin na Majalisar dinkin duniya wanda aka yiwa lakabi da sunan tsohon shugaban majalisar dokokin Jamus Lange Eugene.

Hukumar majalisar dinkin duniyar ta farko da ta fara aiki a birnin na Bonn ita ce hukumar ayyukan sa kai na majalisar, daga bisani kuma aka sami sauran hukumomi na Majalisar dinkin duniyar da suka biyo baya wadanda ke aiki ta fannin raya kasa, muhalli da kuma harkokin lafiya.

Bugu da kari shugaban Majalisar dinkin duniyar Kofi Annan ya kuma yi tsokaci a game da yiwa Majaisar dinkin duniyar kwaskwarima. Yace yunkurin yiwa Majalisar dinkin duniya kwaskwarima wanda ya hada da fadada wakilcin kwamitin tsaro yana da matukar muhimmanci, yace to amma dukkan wata kwaskwarima ga Majalisar dinkin duniya ba za ta cika ba, ba tare da yin gyaran fuska ga kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniyar ba.

Ita kuwa a nata jawabin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi, birnin Bonn ba wai ya rike matsayin cibiya ga hukumomi na kasa da kasa bane kawai, amma shi kan sa yana aiwatar da muhimman ayyukan cigaba. Alal misali ta ce birnin na Bonn ya karbi bakuncin babban taro na duniya kan yanayin muhalli a shekarun 1999 da kuma shekara ta 2001 da taron cigaban kasar Afghanistan dana inganta albarkatun ruwa da kuma babban taro na duniya kan sabbin dabarun makamashi da taro na baya bayan nan da aka gudanar a bana a game da matakan fadakarwa dangane da aukuwar balaoi daga Indallahi.

Ta ce birnin Bonn na amfani da damar da ya samu don zama cibiyar kwararru ta tarayyar Jamus musamman a game da alámura da suka shafi makomar rayuwar alúma tare da yin aiki kafada da kafada da takwarorin su na kasashen duniya.