1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗe taron ƙasashen duniya kan tsaro a birnin Munich

February 3, 2012

Rikicin kuɗi a duniya ka iya yin mummunan tasiri ga sha'anin tsaro da aikin wanzar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/13wW1
German Foreign Minister Guido Westerwelle delivers a statement during the Conference on Security Policy, on Friday, Feb. 3, 2012 in Munich. Uncertainty over the future of the Middle East and the implications of the financial crisis in Europe loom large as top security and defense officials gather in Munich this weekend. The Munich Security Conference, now in its 48th year, begins Friday with officials from more than 70 countries expected to include U.S. Secretary of State Hillary Rodham Clinton and Defense Secretary Leon Panetta, Russian Foreign Minister Sergey Lavrov, German Defense Minister Thomas de Maiziere, French Foreign Minister Alain Juppe, EU foreign policy chief Catherine Ashton. (Foto:Matthias Schrader/AP/dapd)
Guido Westerwelle na daga cikin waɗanda suka fara yin jawabi a gaban taron na MunichHoto: dapd

Yayin da aka buɗe babban taron duniya kan sha'anin tsaro karo na 48 a birnin Munich na nan ƙasar Jamus, shugaban taron Wolfgang Ischinger yayi gargaɗi game da tasirin da rikicin kuɗi na ƙasa da ƙasa ka iya yiwa harkokin tsaro. Ya ce manufar tsaro a wannan ƙarni na 21 ba ta nufin aikin kare ƙasa kaɗai, a'a ta kai ga ba da gudunmawar tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a duniya baki ɗaya. Ciki har da kyawawan manufofin raya ƙasa wanda wani lokaci yake zama tilas a girke sojoji a ƙasashen da ba na su ba, wanda hakan ke cin maƙudan kuɗaɗe. Ya ce idan ƙasashen yamma suka gaza wajen tabbatar da zaman lafiya saboda basussukan dake kansu, to da akwai haɗarin fuskantar rashin kwanciyar hankali a cikin gida. Taron da za a ɗauki kwanaki uku ana yi, yana samun halarcin wakilai 350 daga fannonin siyasa, aikin soja, tattalin arziki da kuma kungiyoyin farar hula.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi