An buƙaci a dakatar rikicin Siriya nan take
April 10, 2012Wakilin MDD da ƙasashen Larabawa rikicin Siriya Kofi Annan ya buƙaci da a tsagaita wuta nan take a Siriya. Kofi Annan yace kada a yi wasti da shirinsa na dakatar da buɗe wuta. Kofi Annan yana magane ne a wani sansanin yan gudun hijiran Siriya dake cikin ƙasar Turkiya, inda yace hukumomin Damaskus na da lokaci nan da ranar Alhamis su yi aiki da starin da ya gabatar. Ko dayake hukumomin Siriya sun janye sojoji daga wasu sassan ƙasar, amma kawo yanzu hankali bai kwantaba, musamman inda masu neman kifar da gwamnati suka fi ƙarfi. A yan kwannan ne dai ake saran kwamitin sulhu na MDD zai yi zama kan lamarin. Masu neman kifar da gwamnatin Bashar Al-assad sun bada rahotonnin cewa har yanzu ana kai farmaki a biranen da suka fi ƙarfi, inda sukace aƙalla mutane 27 sun mutu. Rasha dai ta sake baiwa Siriya ƙarin wa'adi na yin biyya ga tsagaita wutan. Ita ma dai MDD a yammacin talata nan ta fidda sanarwar neman a tsagaita wuta nan take a rikicin na Siriya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Muhammed Abubakar