1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bada sakamakon zaɓen raba gardama a Masar

March 20, 2011

Sakamakon farko ya bayana cewar kashi 70 cikin ɗari na al´umar Masar sun amince da saban kudin tsarin mulki

https://p.dw.com/p/10d3B
Zaɓen raba gardama a MasarHoto: dapd

Hukumomin shari´a a ƙasar Masar sun bayyana sakamakon zaɓen raba gardama da a aka shirya jiya Lahadi, domin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki.

A cewar wani rahoto daga ma´ aikatar shari´a, kimanin kashi 70 ne cikin ɗari, na mutanen da su ka kaɗa ƙuri´a, su ka amince da saban kudin tsarin mulkin.

Jam´iyar ´yan uwa musulmi da jam´iyar PND ta hamɓararren shugaban ƙasa Osni Mubarack sun yi kira ga magoya bayansu su amince da wannan kudi.

A yayin da Mohamed El Baradei ɗan takara shugaban ƙasa mai buƙatar cenji ya nuna da shi.

Idan dai sakamakon ya tabbata, al´umar Masar za ta shirya zaɓen ´yan majalisar dokoki a watan Satumba na wannan shekara.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal