1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da yiwa wasu sassa na tsarin mulkin Masar kwaskwarima

February 9, 2011

An yi garagɗi game da wani juyin mulkin soji, idan tattaunawar da ake yi da 'yan adawa game da sauyin shugabanci kan hanyar da ta dace, ta ruguje.

https://p.dw.com/p/10EmZ
Babu sassautawa a zanga-zangar neman Mubarak ya saukaHoto: picture alliance/dpa

Ɗaruruwan Masarawa masu fafatukar girke demokuraɗiyya sun yi ƙoƙarin toshen harabar majalisar dokoki a wannan Laraba, yayin da wasu dubbanne suka ci-gaba da gangami a dandalin Tahrir dake binin Alƙahira, kwanaki 16 a jere. Kwamitin da aka kafa domin yi wa kundin tsarin mulkin Masar kwaskwarima, ya amince da yi wa wasu sassa guda shida gyare-gyare. Ciki har da yawan wa'adin shugabanci da kuma faɗaɗa yawan masu neman tsayawa takarar neman shugabancin ƙasar. Waɗannan dai na daga cikin muhimman buƙatun 'yan adawa. A kuma halin da ake ciki ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yi kira ga Masar da ta gaggauta aiwatar da canje-canjen da ta alƙawarta.

"Na farko shi ne a ɗage dokar ta-ɓaci, na biyu a kawo ƙarshen tursasawa masu zanga-zanga da 'yan jarida ko a ɓoye ko a bayyane, na uku a sako dukkan firsinonin siyasa sannan na huɗu a aiwatar da canje-canje ga kundin tsarin mulkin ƙasa."

Tun da farko dai mataimakin shugaban Masar Omar Suleiman ya yi garagɗi game da wani juyin mulkin soji, idan tattaunawar da ake yi da 'yan adawa game da sauyin shugabanci kan hanyar da ta dace, ta ruguje. A lokaci ɗaya kuma mataimakin shugaban ya soki dubban masu zanga-zangar da rashin girmama shugaba Hosni Mubarak. Ya ce duk wanda ya nuna buƙatar Mubarak yayi murabus nan-take kuma ya fice daga ƙasar, to tamkar ɓatanci yayi ga shugaban da ma al'umar Masar baki ɗaya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal