1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da tsagaita wuta a Libiya

August 21, 2020

Bangarorin da ke gaba da juna a kasar Libiya sun sanar da amincewa da matakin maida wuka kube, a rikicin kasar da aka kwashe shekaru ana zubar da jini.

https://p.dw.com/p/3hJHK
Libyen Minsterpräsident Fayiz as-Sarradsch
Hoto: AFP

A wannan Juma'ar ce gwamnatin kasar Libiya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, ta sanar da tsagaita buda wuta a fadin kasar tare da kiran janye sojoji musamman a birnin Sirte, yankin da mayakan tawaye suka mamaye.

A wata sanarwa ta daban, bangaren majalisar dokokin Libiya mai hamayya da jagorancin gwamnati ma ya yi kiran a tsagaita buda wutar.

Dukkanin bangarorin biyu na bayyana hakan ne a lokacin da fargaba ke karuwa kan yiwuwar rincabewar al'amura a rikicin na Libiya da aka kwashe shekaru tara ana gwabzawa.

Fayyez al-Sarraj da ke jagorantar gwamnatin ta Libiya, ya sanar da cewar za a yi zaben shugaban kasa da na 'yan majlisa a Libiyar cikin watan Maris na badi.