1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Laifukan yaki kan fararen hula

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 3, 2021

Sojojin Habasha da na Iritiriya da na mayakan TPLF, sun aikata laifukan yaki a kasar da yaki ya daidaita.

https://p.dw.com/p/42Xbg
Äthiopien Mekele | Pro-TPLF Rebellen
Mayakan yankin Tigray na Habasha, na shirin kwace kasarHoto: YASUYOSHI CHIBA/AFP

Wannan dai na kunshe ne cikin wani rahoton hadin gwiwa da ofishin Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya da kuma tsarin dokokin kare hakkin dan Adam na kasar Habasha suka bayar a Geneva. Hakan dai ya biyo bayan wani bincike da suka gudanar, inda suka bayyana cewa an aikata kisan ba gaira da fyade da musgunawa da cin zarafi da azabtarwa a kan fararen hula. Rahoton ya nunar da cewa sojojin gwamnatin Habashan da na makwabciyarta Iritiriya da kuma sojojin mayakan yankin Tigray TPLF da kawayensu ne suka aikata wadannan munanan ayyukan a yakin kasar da ke yankin Kahon Afirka da yaki ci yaki cinyewa. Mayakan na TPLF dai na ci gaba da samun nasara a kan dakarun gwamnati, abin da ya sanya mahukuntan Habashan saka dokar ta baci tare da bukatar al'umma su dauki makamai domin su kare kansu daga mayakan na TPLF.