1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka za ta shiga tsakanin bangarorin Sudan

Binta Aliyu Zurmi
July 24, 2024

Mahukunta a Amurka sun sanar da gayyatar bangarorin da ke gaba da juna a kasar Sudan domin hawa teburin sulhu da zai kawo karshen yakin da suke yi da juna.

https://p.dw.com/p/4ieZw
Sudan | die Generäle Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan und Mohamed Hamdan Dagalo
Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Tattaunawar da Amurka za ta jagoranta, za ta gudana ne a Switzerland a ranar 14 ga watan Augusta, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sauran wasu manyan jami'an diplomasiyar Amurka za su kasance daga cikin masu shiga tsakani.

Shugaban rundunar RSF Mohamed Hamdan Daglo ya amsa goron gayyatar tataunawar, inda ya tabbatar da halartar wakilan bangarensa.

A baya an gudanar da tattaunawa makamanciyar wannan a birnin Jedda na Saudi Arabia a kokari na kawo karshen wannan yaki amma hakar bata cimma ruwa ba.

An shafe sama da shekara guda ana gwabza kazamin fada a tsakanin sojojin da ke karkashin babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun kar-ta-kwana na RSF karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo.

Dubban mutane ne wannan rikicin ya yi sanadiyan salwantar rayukansu yayin da sama da mutum miliyan 10 rikicin ya kuma raba da matsugunnensu.

 

Karin Bayani: Rabin al'umar Sudan na fama da ja'ibar yunwa