1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Amurka da Ukraine na son a yi taron dangi kan Rasha

September 20, 2023

Shugabannin kasashen Amurka da Ukraine, sun yi kiran taron Majalisar Dinkin Duniya da ta tsaya don ganin an yi maganin Rasha kan mamayar da ta kai wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4WaAy
Taron MDD | Joe Biden
Shugaban Amurka, Joe BidenHoto: Mike Segar/REUTERS

Shugaba Joe Biden na kasar Amurka da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, sun gabatar da jawabai masu karfi a babban taron kasashe na Majalisar Dinkin Duniya, inda suka bukaci hadin kan shugabanni a kan yaki da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

Cikin kalamansa a taron, Shugaba Biden ya ce Rasha na ganin duniya za ta ci gaba da fargabar da za ta ba ta damar cinzalin Ukraine ba tare da wata turjiya ba.

Shugaban na Amurka ya kuma tambayi mahalarta taron, ko idan aka kyale Ukraine cikin wannan hali akwai wata kasar da za ta tsira?

Daga nashi bangare, Shugaba Zelenskyy na Ukraine wanda ke halartar taron na MDD a karon farko a zahiri, bukatar taron dangi ya mika wa kasashen duniya kan halin da kasar tasa ta fada.