1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty International ta ce an aikata ta'asa akan bil Adama a Siriya

July 6, 2011

Gwamnatin Siriya na ci-gaba da ɗaukar matakan murƙushe masu zanga-zangar ƙyamar shugaba Bashar al-Assad.

https://p.dw.com/p/11qYc
Hoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar kare haƙin bil Adama ta ƙasa da ƙasa wato Amnesty International ta fid da wani rahoto dake bayani dalla dalla game da zargin dakarun ƙasar Siriya da aikata mummunar ta'asa akan ɗan Adam. Rahoton ya ce mutane da dama sun mutu a hannun jami'an tsaro, sannan an ci zarafin maza fararen hula lokacin da aka yiwa masu zanga-zanga ƙawanya watanni biyu da suka wuce. Cilina Nasser wakiliyar Amnesty International a birnin Beirut ta yi kira ga kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta laifukan yaƙi da ta gudanar da bincike akan waɗannan zarge-zarge.

"Zanga-zanga ce ta lumana bisa fina-finan bidiyon da muka gani. Mun san cewa a ranar 27 ga watan Afrilu an halaka dakarun tsaro guda biyu. Amma zancen gaskiya shi ne ko da an samu masu ɗauke da makami a Tel Kalakh, dole ne dakarun tsaron Siriya su girmama hakin ɗan Adam da tabbatar da tsaron jama'a a matakan da suka ɗauka."

Har ya zuwa wannan Larabar gwamnatin Siriya na ci-gaba da murƙushe masu zanga-zanga, inda aka halaka mutane 22 a birnin Hama dale tsakiar ƙasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal