1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty: Hukunci kisa ya karu a duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
May 24, 2022

Cikin rahotonta na shekara, kungiyar Amnesty International ta ce Chaina da Iran na kan gaba wajen aiwatar da hukunci kisa a duniya a shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/4Bn9W
Symbolbild I Justiz I Todesstrafe
Hoto: Steve Helber/AP/picture alliance

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa adadin hukuncin kisa ya sake karuwa a duniya a cikin shekarar da ta gabata. A cikin rahotonta a kan hukuncin kisa na shekarar 2021, Kungiyar ta ce kawo karshen takunkumin corona ya sa an sake komawa gidan jiya, inda ta lissafo akalla hukuncin kisa 579 a cikin kasashe 18 - adadin da ya karu da kashi 5% idan aka kwatanta da shekara ta 2020.

Yawancin kashe-kashen mai yiwuwa sun faru ne a kasar Chaina, in ji Amnesty, duk da cewa gwamnatin kasar na daukar bayanan kisa a matsayin sirrin kasa. Amma kuma Iran ta kasance a sahun gaba wajen aiwatar da hukuncin kisa a kan akalla mutane 314.