1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta kwashe jama'arta da ke Nijar

August 3, 2023

Yayin da kasashe ke ci gaba da kwashe jama'arsu daga Nijar bayan juyin mulkin, gwamnatin Amirka ta bayar da sanarwar fara kwaso ma'aikatan offishin jakadancinta da ke kasar.

https://p.dw.com/p/4UiEE
Niger I Fluggäste vor dem internationalen Flughafen Diori Hamani in Niamey
Hoto: AFP

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Amirka ta ce, ta fara shirin kwashe ma'aikatanta da ba su yin aikin kai daukin agajin gaggawa da kuma iyalan da suke offishin jakadancinta da ke birnin Yammai.

Kakakin ma'aikatar, Matthew Miller ya ce, offishin zai kasance a bude domin gudanar da wasu ayyukan gaggawa da za su iya tasowa. Tuni dai gwamnatin Washington ta shawarci Amirkawa da su kaurace wa yin balaguro zuwa Nijar.

A makon da ya gabata ne sojoji suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, inda suka kifar da gwamnatin farar hula ta shugaba Mohamed Bazoum.