1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai janye takunkumi kan Turkiyya

Binta Aliyu Zurmi
October 23, 2019

Kamfanin dillancin labaran Jamus na (DPA) ya ruwaito cewar, shugaban Amirka Donald Trump ya ce zai janye takunkumin tattalin arziki da ya kakabawa Turkiyya bisa fadan da take yi da Kurdawa a Siriya.

https://p.dw.com/p/3Ro0C
US-Präsident Trump gibt im Weißen Haus in Washington eine Erklärung zum Konflikt in Syrien ab
Hoto: AFP/S. Loeb

Shugaban  Trump ya ce zai yi hakan ne bisa alkawarin da Turkiyya ta yi na tsagaita wuta.

A wata sanarwa da ta fito daga fadar White House, Mr Trump ya kare matakin janye sojojin kasarsa da ya yi inda ya ce Amirka ba 'yar sandan duniya ba ce, yana mai cewa sun yi nasu kokarin yanzu kuma lokaci ya yi da wata kasar zata bada nata gudumawar.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar tsaro ta NATO ke kokarin kawo karshen rikicin kasar Siriya baki daya.