1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta ɗaga wa Sudan kafa

October 20, 2020

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce za soke sunan ƙasar Sudan daga cikin ƙasashe masu ɗaukar nauyin ta'addanci muddin ta amince da dawo da hulɗa da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/3kA9k
Walter Reed Militärhospital | Donald Trump Videobotschaft Covid-19
Hoto: The White House via Reuters

Shugaban na Amirka ya ce wani sharaɗin soke sunan Sudan daga jerin ƙasashen, shi ne ta amince da biyan diyyar dala miliyon 335 ga wasu Amirkawa da hare-haren ta'addanci suka shafa a shekara ta 1998.

Cikin watan jiya ne ƙasashen Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, suka dawo da dangantaka tsakaninsu da ƙasar Isra'ila, lamarin da ya sanya Amirka sanya Sudan ɗin daga cikin ƙasashen da za su biyo.

Sanya Sudan cikin jerin ƙasashen da ke ɗaukar nauyin ta'addancin dai ya haddasa mata koma baya ta fuskar tattalin arziki, duk da kasancewar tana ɗaya daga cikin ƙasashe masu ƙarancin ƙarfi.

Tuni ma dai Firaminista mai riƙon gwamnatin Sudan, Abdalla Hamdok, ya gode wa Shugaban na Amirka a shafinsa na twitter, bayan sanawar.